Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Al’ummar garin Rimin Zakara dake jihar Kano, maza da mata, sun fito domin bayyana damuwarsu kan rashin biyan su diyyar gonaki da gidajensu, sakamakon aikin titin jirgin kasa da gwamnatin tarayya ta ayyana.
Tun sama da shekara guda da gwamnati ta sanar da fara wannan aiki tare da alkawarin biyan diyyar, amma har yanzu ba a biya su ba, duk da kokarin da suka yi na neman hakkinsu.
Malam Hassan Hamza Rimin Zakara, jagoran wannan al’umma, ya bayyana cewa sun dade suna kira ga gwamnati kan wannan lamari, amma babu wani ci gaba. Ya ce, tun da ba a biya su hakkin su ba, ba su da wani zabi illa su ci gaba da gudanar da nomansu a kan wadannan filaye.
Hakazalika, mai unguwar Rimin Zakara, Alhaji Yakubu Shehe, ya nuna damuwar al’ummarsa kan halin da suke ciki, inda ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su kawo musu daukin gaggawa.
Ya kuma yi kira ga Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya sanya baki domin ganin an biya al’ummar yankin hakkinsu.