An Yi Jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi

Daga Safiyanu Haruna Kutama

Dubban Mutane daga sassan Najeriya ne suka Halarci Jana’izar Shaik Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi wanda Allah ya yi wa rasuwa a daren  Juma’a.

An gudanar da Jana’izar ne a Masallacin idi na Game Village dake garin Bauchi.

Shaik Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi dai ya rasu yana da Shekaru 68.

ya bar ‘ya’ya 38 da jikoki da Dama Kuma matan sa 3.

Manyan Yan siyasa irin su tsohon matemakin shugaban Nigeriya Atiku Abubakar da kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’iqamatus Sunna JIBWIS da sauran manyan malamai tuni suka fara aikewa da sakon ta’aziyya tare da alhinin rasuwar sa.

Post masu alaƙa

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP 

Kotun musulunci dake Jogana ta bayar da umarnin tsare mutanen da Ake tuhuma da yunkurin aikata tsafi.

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM.