Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Al’ummar garin Gano dake karamar hukumar Dawakin Kudu, sun yi wa gwamnatin Kano Al-Qunut, kan zargin ta da yunkurin kwace musu Gonaki.
Mutanen sun gudanar da Sallah tare da yin addu’o’in neman dauki daga Ubangiji.
Magidanta, maza da mata hadi da samari ne suka halarci taron addu’ar daya gudana a safiyar yau Litinin.
- Sakacin Jami’an Mu Ne Ya Sa Bindigogi Ɓacewa- ‘Yan Sanda
- ‘Yan Jam’iyyar PDP Da AAC Sun Koma APC A Zamfara
Mutanen sun ce gwamnatin tana son kwace musu gonakin da girman su yakai kilomita 5 don yin aiki a wajen. Haka ne yasa al’ummar rokon gwamnatin tayi hakuri ta bar musu filayen su.