Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Rahotanni daga jihar Zamfara Arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu magoya bayan jam’iyyun adawa na AAC da PDP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Rahoton jaridar Leadership, ya bayyana cewa jam’iyyun na AAC da PDP sun samu koma baya sakamakon ficewar mambobin nasu zuwa APC.
Shugabancin APC na Zamfara ne ya karbi mutanen lokacin wani taron da aka gudanar a ranar asabar data gabata.
- Isra’ila Na Shan Caccaka Kan Hana Shiga Da Abinci Gaza
- An Kama Ɗan Ƙasar Angola Kan Safarar Miyagun Kwayoyi A Najeriya
Cikin mutanen da suka canja shekar akwai dan takarar gwamnan Zamfara na jam’iyyar AAC a zaben shekarar 2023, Muhammad Kabir Sani, da tsohon dan takarar majalisar dokokin jihar na PDP.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Alhaji Isiyaka Ajiya Anka, shine ya karbi sauyin shekar mutanen.