• Home  
  • Ana Ci Gaba Da Tattara Sakamakon Zaben Gwamna A Anambra
- Babban Labari - Labarai

Ana Ci Gaba Da Tattara Sakamakon Zaben Gwamna A Anambra

Tuni aka kammala kaɗa ƙuri’a a kusan dukkan rumfunan zaɓen da ke jihar Anambra yayin da sama da mutum miliyan biyu ke zaɓen sabon gwamnan jihar. Abin da ya rage yanzu shi ne warewa da ƙirga ƙuri’un, wanda shi ma an kammla a wurare da dama. Hukumar zaɓe Inec na ci gaba da tattara sakamakon […]

Tuni aka kammala kaɗa ƙuri’a a kusan dukkan rumfunan zaɓen da ke jihar Anambra yayin da sama da mutum miliyan biyu ke zaɓen sabon gwamnan jihar.

Abin da ya rage yanzu shi ne warewa da ƙirga ƙuri’un, wanda shi ma an kammla a wurare da dama.

Hukumar zaɓe Inec na ci gaba da tattara sakamakon a matakin ƙananan hukumomin jihar 21 domin ƙirgawa da sanar da wanda ya yi nasara.

Zuwa yanzu Inec ta wallafa kashi 86.10 cikin 100 na sakamakon zaɓen a shafinta na intanet IReV. Ma’ana ta wallafa sakamako 4,925 cikin jimillar 5,720 da ake buƙata.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai