Hukumar wayar da kan jama’a ta Nijeriya NOA, ta bayyana gamsuwarta kan yadda yan kasar ke ci gaba da taimaka mata wajen wayar da kan al’umma akan abinda ya shafi tsaro.
Hukuma ta ce cikin watanni uku, ta kara kaimi wajen wayar da kai, inda adadin ya kai sama da mutane miliyan talatin da biyu.
Darakta Janar na Hukumar NOA, Mallam Lenre Issa-Onilu, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar tare da hukumomin tsaro, Soji, DSS, NDLEA da sauransu na shekarar 2025 a birnin tarayya Abuja.
NOA ta kara da cewa yan Nijeriya suna bayar da gudunmawa sosai ta hanyar tallafawa hukumomin tsaro da bayanan sirri wadanda suke taimaka wajen magance matsalar tsaro.
Mallam Lenre Onilu, ya ce hukumar ta wayar da kan jama’a kan abubuwan da suka shafi tsaro a dukkan jahohin Nijeriya 36 ciki harda Abuja.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa gidajen Talebijin da Radiyo sama da 50 sun yadawa al’umma hanyoyin da za su kula da duk wani abu da ya danganci tsaro, ga yan Nijeriya kimanin miliyan 29, sannan kuma hukumar ta ce wadanda suka amfani da wayar da kan ta shafukan sada zumunta sun mutane miliyan 200.
