Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci.
Barau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame ta ba.
“Shugaban Amurka ya fito ya ce, ‘Najeriya wulaƙantaciyyar ƙasa ce, za mu kai muku hari,’ wannan bai dace ba.
“Ya kamata ya janye wannan maganar ya kuma nemi afuwar Najeriya,” in ji Barau.
- NOA Ta Bayyana Gamsuwarta Kan Yadda Jama’a Ke Taimakamata Ta Hanyar Wayar Da Kai
- Tinubu Ya Gana Da Shugaban Ƙasar Saliyo A Abuja
Ya ƙara da cewa maganganun Trump sun karya dokokin diflomasiyya da na ƙasa da ƙasa.
“Idan kuna da ƙorafi a kan ƙasarmu, ku bi hanyoyin shari’a. Ku je Majalisar Ɗinkin Duniya, ku nemi izini, sannan ku aiwatar da shi yadda ya dace. Tsallake wannan hanya ba abin da ya dace ba ne,” in ji shi.
Barau, ya jaddada cewa kalaman Trump ba za su firgita Najeriya ba, kuma ya kamata shugaban Amurka ya girmama ƙasa mai cin gashin kanta.
“Ba za mu ji tsoron faɗin gaskiya ba. Da Trump yana nan, da na faɗa masa kai-tsaye cewa abin da yake yi ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa kuma ba daidai ba ne,” in ji shi.

