Home » APC Na Zanga-zangar Ƙalubalantar Sakamakon Zaɓen Gwamnan Kano

APC Na Zanga-zangar Ƙalubalantar Sakamakon Zaɓen Gwamnan Kano

by Anas Dansalma
0 comment

Jam’iyyar APC da magoya bayanta a yau na gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen gwamnan Kano a ofishin hukumar zaɓen ta ƙasa reshen jihar Kano.
Wannan zanga-zanga dai ana yin ta ne domin nuna ƙin amincewa da ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen na jihar Kano.
Majiyarmu ta rawaito mana yadda matasa ɗauke da kwalaye suka cika wasu titunan tare da yin waƙe-waƙe na habaici da nuna rashin jin daɗi.
Sai dai wasu da ake zargin yan ta’adda ne sun yi amfani da wannan dama wajen tilasta wa ‘yan kasuwa rufe wuraren sana’o’insu.

Shi ma ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar ta APC, a yayin wata ganawa da manema labarai a jiya, ya bayyana cewa kamata ya yi hukumar zaɓe ta ƙasa ta sanar da zaɓen gwamnan a matsayin wanda bai kammala ba, wato inconclusive.
Tare da yin zargin cewa Abba bai lashe zaɓen da aka hukumar zaɓen ta sanar da cewa shi ya lashe ba.
Sai dai kuma a ɓangaren jam’iyyar NNPP, ta bakin shugaban jam’iyyar, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa suna zargin gwmnatin jihar Kano ne ma da assasa tashe-tashen hankula saboda sun gano faɗuwa.
Don haka, a ganinsa wannan ba abin mamaki ba ne.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi