APC ta fara faɗawa tarkon rikici a jihar Kano

Kurar rikici ta fara turnuƙewa a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, da ke arewacin Najeriya, makonni bayan sauyin sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf.

An fara ganin ƙurar ne a tarukan haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar APC tsoffi da sabbi a cikin wasu ƙananan hukumomin jihar.

Shugabancin APC ne ya ba da umarnin gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a wani mataki na ɗinke duk wata ɓaraka gabanin babban zaɓen jam’iyyar da ke tafe.

Dama dai tun da farko masana siyasa a Najeriya sun yi hasashen samun rikici a tsakanin ƴaƴan jam’iyyar APC musamman bayan shigowar gwamna Abba Kabir Yusuf.

Rahotanni na cewa an samu musayar yawu da cecekuce a yayin taron masu ruwa da tsaki a matakin kananan hukumomi.

Na baya-bayan nan shi ne taruka biyu da aka yi a karamar hukumar Kano Municipal inda ɓangaren da ke biyayya ga tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ƙarƙashin jagorancin Muntari Ishaq Yakasai da Baffa Babba Dan Agundi da Injiniya Sagir Koki, suka yi nasu taron.

A bangare guda kuma, bangaren da ke biyayya ga sanata Barau Jibril, karkashin jagorancin Salisu Maje Ahmed Gwangwazo, wato Alhajin Baba da sauran kusoshi, su ma sun gudanar da nasu taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *