Home » APC Ta Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓen Gwaman Jihar Kano

APC Ta Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓen Gwaman Jihar Kano

by Anas Dansalma
0 comment
APC ta jihar kano ta yi fatali da zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar din data gabata, tare da bukatar hukumar zabe data soke zaɓen ta kuma sake shirya wani zaben.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar kano Alhaji Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan lokacin taron manema labarai wanda ya gudana a ofishin yaƙin neman zaben jam’iyyar APC a nan kano.
 Abdullahi Abbas wanda mai bai wa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a Barr. Abdul Adamu Fagge ya wakilta ya ce zaɓen da aka gudanar a ranar asabar 18 ga watan Maris akwai kura-kurai a cikinsa,
Sannan jami’in tattara sakamakon zabe bai bi ka’idojin da ya kamata ba wajen bayyana sakamakon zaɓen.
 Akwai mazabun da aka samu hatsaniya da kuma Inda aka samu sanya kuri’u fiye da ƙima a akwatuna, a irin wannan yanayin da aka kuri’un da aka ce anyi nasara da su basu kai wadanda aka soke ba, don haka bai kamata a ayyana wanda ya lashe zaben ba, kamata yayin zaɓen ya zama wanda bai kammala ba a cewar Abdullahi Abbas
 Ya ƙara da cewa, irin abin da ya faru a Kano shi ne ya faru a jihohin Adamawa da Kebbi, kuma a can an bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba, amma kuma aka bayyana sakamakon zaben na Kano wanda hakan ya sabawa dokar Zaɓe.
 Sakamakon faruwar abun da akai mana yanzu haka mun tattara lauyoyin mu domin su yi nazari a kan wannan sakamakon da ya bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, daga nan kuma za mu tafi kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaben.  
 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi