Tsohon shugaban ƙasar nan Mahamadu Buhari ya yaba wa gwamnatinsa game da irin rawar da ta taka wajen kare ƙasar daga bala’in cin hanci.
Buhari yace sun yaƙi cin hanci da rashawa fiye da ko wace gwamnatin da aka taɓa yi a kasar nan tunda aka koma dimokradiyya a shekarar 1999.
Tsohon shugaban ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Garba Shehu a jiya Lahadi da ya ke mayar da martani ga sukan lamirinda tsohon ministan shari’a Mohammed Bello Adoke ya yi cewa gwamnatin Buharin ita ce mafi gazawa a tarihin Najeriya, Buhari yace sukan lamirin da tsohon ministan ya yi, ya samo asali ne daga gwamnatinsu ta PDP ta tsohon shugaban ƙasa Dokta Goodluck Ebele Jonathan.
Haka kuma tsohon shugaban ƙasar Mahamadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan sojoji a Neja kuma yace ya tabbata jami’an tsaro za su yi nasara akan ‘yan ta’adda.