Tsohon Ƙaramin Ministan Gidaje da ƙawata Birane Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya bayyana cewa tun kafin a sauke shi shugaba Tinubu ya sanar dashi.
Tohon ministan ya ƙara da cewa cire shi ko kusa ko alama bashi da alaƙa da rashin ƙoƙari.
T Gwarzo ya ƙara da cewa Tinubu ya sanar dashi suna buƙatar samun wani Ministan daga yankin Kano ta tsakiya.
“Na yi ƙokarin ba da shawara ga lamarin amma dai abun bai yiwu ba, amma cire ni bashi da alaka da rashin ƙoƙari” a cewar tsohon mataimakin gwamnan.
T Gwarzo dai na daga cikin ministocin da shugaba Tinubu ya sauke, duk da ana ganin yana daga cikin makusantan shugaban ƙasar ta fannin siyasa, inda ya maye gurbin sa da Abdullahi Yusuf Ata shine daga yankin Kano ta tsakiya.