Home » ba mu da kudin biyan tallafin wutar lantarki a Najeriya ~ Nasiru El-Rufa’i

ba mu da kudin biyan tallafin wutar lantarki a Najeriya ~ Nasiru El-Rufa’i

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Nasiru El-Rufa'i

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya ce ba zai yiwu Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da bayar da tallafi ga ɓangaren wutar lantarki ba.

El-Rufa’i ya faɗi hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban Majalisar Dattijai domin tantance shi a matsayin Minista.

A makon da ya gabata ne dai Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan El-Rufa’in da wasu mutum 27 ga Majalisar da yake neman nadawa a matsayin Ministoci.

Elrufa;i Ya ce gwamnatin ta shafe shekara da shekaru tana biyan tallafin ga bangaren, amma yanzu ya ce ba abu ba ne mai dorewa.

Ya ce, Najeriya tana da na’urorin da za su iya samar da kusan megawat 13,000 na wutar lantarki, amma abin da take samarwa bai wuce megawat 4,000 zuwa 5,000 ba.

Yaƙara da cewar, Matsalar a bangaren iskar gas take, kusan shekara 10 ke nan ana bayar da tallafin wutar lantarki, wannan ba abu mai yiwuwa ba ne kuma ba za mu amince da shi ba.

“Mun yi bincike a kan kamfanonin rarraba hasken lantarki, amma masu aiki daga ciki ba su wuce guda uku ba.

Sauran aikinsu duka sama-sama ne. Shugaban Kasa na da tanadin da nan da shekara 7, matsalar wutar lantarki za ta zama tarihi a Najeriya.

Shugaban Kasa ya damu matuka cewa makwabtanmu kasashe iri su Nijar da Jamhuriyar Benin ba sa fama da wannan matsalar,” in ji shi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?