Home » An bukaci shugaban Najeriya da ya kara harajin taba sigari

An bukaci shugaban Najeriya da ya kara harajin taba sigari

by Anas Dansalma
0 comment
Wata Kungiya ta bukaci shugaban kasar Najeriya da ya kara harajin taba sigari

Wata Kungiya mai zaman kanta mai suna Civil Society Legislative Advocacy Centre, CISLAC ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta fito da tsare-tsaren da za su tabbatar da karin kudin harajin taba sigari a Najeriya.

Anyi.

Babban Daraktan kungiyar Auwal Ibrahim Rafsanjani wanda Solomon Adoga, Babban Jami’in Shirye-Shirye na kungiyar ya wakilta ne yai wannan kiran inda ya ce,

Daga cikin ikin manufofin da shugaba Tinubu ya yi yaƙin neman zabe da su, ya yi alkawarin kara yawan kudaden kula da lafiya a kasar nan ta hanyar inganta kasafin kuɗi da kuma tantance harajin amfani da kayayyaki masu cutarwa irin su taba da barasa.

Ya kuma ƙara da cewa taron na ƙoƙarin tunatar da shugaban kasa ne muhimmancin cika wannan alkawari da yayi lokacin yakin neman zabe.

Ya kara da cewa, akwai bukatar gwamnati ta ƙara kudaden haraji ga kayan da ke cutar da al’umma musamman taba sigari da barasa domin takaita masu shan taba da barasa da kuma samar da karin kudaden ga fannin kula da lafiyar al’umma.

Ya ce sun shafi shekaru da dama suna fafutuka domin a inganta tsarin harajin taba sigari a ƙasar yana mai cewa tsarin kara kudaden harajin taba ita ce hanyar mafi sauki da za’a takaita shan taba sigarin da kuma inganta tattalin arzikin kasa don al’umma su amfana.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi