Home » Babban Daraktan Hukumar Leƙen Asiri ta Kasa (NIA) Ya Yi Murabus

Babban Daraktan Hukumar Leƙen Asiri ta Kasa (NIA) Ya Yi Murabus

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar, ya yi murabus. 

Baban daraktan na NIA da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shekaru bakwai da suka gabata, ya miƙa takardar murabus ɗin ne bayan ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar Asabar.

Da ya ke jawabi bayan taron da ya kawo ƙarshen wa’adin jagorancin hukumar, tsohon shugaban na NIA ya godewa shugaba Tinubu bisa damar da ya samu na yiwa ƙasa hidima.

Ahmed Rufa’i Abubakar ya bayyana cewa ganawarsa da shugaban ƙasa abu ne na yau da kullum, inda ya ƙara da cewa,

“Wannan taro ne na yau da kullum, lokaci zuwa lokaci muna yi wa shugaban ƙasa bayanin halin da ake ciki kuma yau ma haka ne.

“Sai dai bayan kammala taron a yau, na mika takardar ajjiye aiki, sannan kuma shugaban ƙasa ya amince da murabus ɗi na.

“Na gode masa da ya ba ni damar yi wa Najeriya hidima a ƙarƙashin jagorancinsa na kawo sauyi, har na tsawon watanni 15, wanda ba kasafai ake samun irin wannan dama ba.

“Don haka na gode masa sosai, kuma na yi alƙawarin ci gaba da zama mai sadaukar da kai ga ƙasar mu da kuma aikata kyawawan ayyuka.”

Ahmed Rufa’i Abubakar wanda ya ƙi bayyana dalilin murabus din nasa ya ce,

“Akwai dalilai da dama da suke sa mutum ya yi hakan, wasu batutuwa na ƙashin kai ne, wasu kuma buƙatar iyali ne, amma ni nawa dalilin ba wani mai tsanani bane, kuma zumuncin mu zai ci gaba.

“Na tattauna da mai girma shugaban ƙasa, ya fahimce ni sosai, kuma na yi alƙawarin ci gaba da kasancewa tare da al’amurran da suka shafi tsaron ƙasar nan”.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?