Wani matashi mai aikin shara a filin jirgin Malam Aminu da ke Kano ya mayar da Dala Dubu 10 da ya tsinta, kudin da sun kai kimanin Naira miliyan 16, da ya tsinta.
Auwal Ahmed Dankode mai aikin sharan jirgin saman ya tsinci kuɗaɗen ne a cikin jirgin kamfanin EgyptAir, ranar Laraba da karfe 1:30 na rana.
Auwal, wanda ɗan asalin ƙauyen Dankode ne da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ya sanar da shugabannin filin jirgin nan take ya kuma damka wa manajan jirgin kuɗaɗen da ya tsinta.
Mai kudaden da suka zube Balarabe ya zo cigiyar kuɗaɗensa da suka bace, inda manajan kamfanin ya yi masa tambayoyi, daga bisani kuma aka damka masa kudinsa.
Yayin karbar kudin Alh Balarabe ya yi godiya ya kuma bayyana farin ciki har ta kai ga ya rungume mai sharan jirgin da ya tsinci kudin nasa amma ya dawo da su bai boye ba.
Auwal Ahmed Dankode ya ce, “Mutane da yawa a filin jirgin sun daga ni sama suna yaba min bisa abin da nayi.