Wani abu da ake zargin bam ne ya tashi da wani manomi mai suna Isyaku Gambo, a kusa da garin Bassa, da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da manomin ke kan hanyarsa ta kai kayan amfanin gona zuwa Bassa.
Kawo yanzu Ana zargin cewa ’yan ta’adda ne suka dasa bam ɗin a kan hanya tsakanin Unguwan-Usman da Bassa.
Wani mazaunin yankin, ya bayyanawa jaridar Aminiya cewa fashewar bam ɗin ta tarwatsa gawar mamacin gaba ɗaya nan take.
“Lamarin ya faru ne a yau (Asabar) da misalin ƙarfe 3 na rana.
“Mamacin na kan hanyarsa ta dawowa daga gona bayan ya ɗauko kayan amfanin gona.
“Wannan ne karo na farko da muka fuskanci irin wannan a nan. Ana zargin ’yan ta’adda ne suka dasa bam ɗin,” in ji wani mazaunin yankin.
Ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ci tura domin bai amsa kiran waya baya.