Da sunan Allah Mabuwayi, tsira da amincin Sa, su tabbata ga manzon rahama, da iyalan sa, da sahabban sa, da masu koyi da su har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, muqalar mu a yau tana dubi ne akan mulkin siyasa, wanda ake kira da sunan dimokradiyya. A yau muna cikin shekara ta ashirin da biyar a jere da fara wannan tsari a Najeriya.Wato tun bayan karshen mulkin soja na janar Abdussalami Abubakar a shekarar 1999.
Daga wancan lokaci zuwa yau, an yi shugabannin kasa guda biyar, tun daga kan Obasanjo zuwa mai ci a yanzu, Bola Tinubu. Hakanan a matakan jihohi, an yi gwamnoni daban-daban, daga jam’iyyun siyasa mabanbanta.
To kamar yadda ake fadi, ita dimokradiyya gwamnati ce ta jama’a, wadda jama’a suka zaba, kuma don aikin jama’a.
Kenan jama’a sune kashin bayan tafiyar da ita. Sai dai shin mu a tsarin Najeriya, haka abin yake ? Abinda nake nufi da wannan tambaya shine, shin jama’ar da ake dimokradiyyar saboda su, suna ganin amfani ko tasirin ta, ko a’a ? To ni dai a tawa fahimta, akwai matsala a wannan tsari. Domin kuwa mutane ne yan’kadan suke amfanuwa da ita dimokradiyyar.
Yanzu misali ka dauki barin shugaban kasa da rukunan sa (executive).
Zaka ga mutane wanda adadinsu bai wuce mutum 50 da yan’kai ba. In ka dauki bangaren majalisar kasa (legislative) su ma basu kai mutum 600 ba.
Sai kuma bangaren shari’a (judiciary), wanda sune ma suke da dan yawa. Duka dai in ka hada su ba su kai mutum miliyan 1 ba, a kasar da ke da mutum sama da miliyan 200. To amma sai kaga suke da kusan kashi 50 ko ma fiye na kasafin kudin kasa.
Sai kaji an ce dan majalisa na da kudin sabuwar mota, rigar shiga ofis, kudin fara aiki, kudin jarida, kudin tafiya hutu (recess) da sauran su. Haka shi ma minista, kaji kudade daban-daban. Bangaren shari’a shi ma ga albashi mai tsoka, ga alawus-alawus.
Su kuma ma’aikata da sauran jama’ar kasa su samu sauran kashin.
To ina dimokradiyya a nan? Ai a kyautata albashin ma’aikata da yin ayyukan raya kasa, da zai amfani jama’a shi yakamata aba muhimmanci. Domin in ma’aikaci ya samu kulawa, to mai aikin karfi da mai sana’a, su ma za su samu. Kasancewar za’a bukaci ayyukan su da kayan sayarwar su. Kaga kudi za su watsu cikin jama’a kenan.
Koda yake masu makaman siyasar, na da mataimaka da suke dauka, su sa musu albashi. Amma dai zaka ga cewa, in an kwatanta su da sauran jama’ar kasa, yan’kadan ne su.
Don haka zahirin magana shine, a fuskantar da arzikin kasa wajen tsare-tsaren da zasu gina kasa ta fannoni kamar ilmi, lafiya, aikin gona, masana’antu da sauran su. Hakanan bangaren ruwan sha, lantarki da tituna, suna bukatar kulawa ta gaggawa. Yanzu ka duba koguna da madatsun ruwa da muke dasu a wannan kasa, amma ruwan sha ya na wuya. Ga harkar wutar lantarki, kullum sai dada dagulewa take. Tituna kuwa ba’a magana.
Sai ka ga yawancin garuruwan mu da hanyoyin tafiya gari zuwa gari ba dadi. Kaga ana ta faman hadarin mota saboda munin su.
To kira dai anan shine, ya kamata masu rike da madafun iko (yan’siyasa da jami’an gwamnati) su yi nazari sosai wajan kyautata shugabancin su. Babu shakka dukkannin mu masu kiwo ne, kuma za’a tambaye mu a bisa kiwon da aka bamu (hadisi).
A karshe ina fata Allah ta’ala Ya bamu ikon gyara, Ya yi jangora ga shugabanni, Ya kuma taimaki kasar mu.
Muhammad S. Ahmad
Bayero University, Kano
26/11/ 24