Wasu bama-bamai guda biyu sun tashi a wasu wurare a gundumar Dansadau da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Jaridar PremiumTimes ta ruwaito cewa, bama-baman biyu sun fashe ne akan titin Dansadau zuwa Malamawa dayan kuma a kan titin Malele, duk a gundumar Dansadau.
Wani mazaunin yankin da abin ya faru Nuhu Babangida ya ce wata motar fasinja ce da ke kan hanyar kasuwar mako-mako ta Dansadau a safiyar Juma’a ta taka bam din.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 8,034 A Cikin Watanni 11
- Fararen Hula Dubu 10 Sun Salwanta A Wurin Sojojin Najeriya — Amnesty
Babangida ya ce bama-baman da suka fashe a kan titin Malamawa da Malele sun tashi ne a lokaci guda amma ba a samu asarar rai ba.
Wannan dai shine karo na uku da bam ya tashi a jihar Zamfara, kuma an dora alhakin tada bama-baman akan ‘yan ta’addar lakurawa.