Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi ne zabinsa ba a lokacin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa ba.
Ya yi nuni da cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan shi ne zaɓinsa, amma ya marawa Tinubu baya bayan ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.
Ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai inda ya ce yana da ƴancin goyon bayan duk wanda yake so kafin Shugaba Tinubu ya yi nasara a zaɓen fidda gwanin na shekarar 2022.
Sanata Abdullahi Adamu ya ce, abubuwa da dama sun faru kafin babban taron jam’iyar na ƙasa zuwa ranar da aka gudanar da babban taron sannan yana wajan inda ya jagoranci babban taron jam’iyyar.
Ya kuma ƙara da cewar, Kwana ɗaya bayan zaɓen, ya jagoranci gaba ɗaya ƴan kwamitin gudanarwar jam’iyar zuwa gidan Tinubu a Asokoro, inda ya tabbatar masa da goyon bayan su da cewa za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da shi domin tallata shi a wajen ƴan Najeriya.