Wasu da ake zargin ɓarayi ne sun sace motar ofishin Malam Nuhu Ribadu, mai bai wa shugaban ƙasa shawara a fannin tsaro a wani masallacin juma’a dake birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa an ajiye motar a kusa da wani masallacin birnin tarayya Abuja da misalin ƙarfe 1:05, lokacin da jami’an ofishin Nuhu Ribadu suka je yin sallar juma’a.
Tuni dai jami’an rundunar ƴan sandan Abuja suka fara gudanar da binciken wadanda suka sace motar mai ƙirar Toyota Hilux.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an ofishin na Ribadu sun iske babu motar a wajen da suka ajiye ta yayin da suka kammala Sallar Juma’ar
- UNICEF Ta Nemi Haɗin Kan Al’umma Don Yakar Cutar Polio.
- Yan Sandan Kano Sun Kamo Gungun Yan Dabar Da Suka Yiwa Kansu Raunuka Da Makamai A Kofar Na’isa