Daga: Zubaida Abubakar Ahmad
Sama da ma’aikatan lafiya 20 na asibitin koyarwa na Aminu Kano wdanda sukayi mu’amullah da wata maras lafiya da aka gano da cutar zazzabin Lassa an gano basu dauki wannan cuta ba.
Haka kuma sauran ma’aikatan lafiyar da aka gwada su biyo bayan mu’amullar su da maras lafiyar suma an gano basu da wannan cuta.
Yanzu haka mijin matar da take dauke da cutar shi ne kadai aka gano yana dauke da kwayar cutar ta Lassa.
Shugaban majalisar bada shawara ta aikin likita ta asbitin farfesa Muhammad Abba Suwaid ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a yau asabar.
Yace an killace ma’aikatan asibitin na tsawon kwanaki inda aka debi jinin su aka kuma gwada aka gano basu da wan nan cuta.
Farfesa Muhammad Abba Suwaid ya godewa Allah bisa yadda ma’aikatan lafiya suka tsallake rijiya da baya biyo bayan rashin daukar wannan cuta.
Ya kuma yabawa ma’aikatan kan yadda suke gudanar da aikin su cikin kishi da kwarewa wajen kula da marasa lafiya a asibitin.
Shuagaban majalisar ya bayyana cewa hukumar asibitin ta sami labarin wata mata mai juna biyu yar shekara 22 da aka kawo asibitin a ranar 5 ga watan afirilu tana dauke da cutar ta zazzabin lassa.Yayi bayanin cewa nan da nan hukumar asibitin ta dauki matakan kariya na gaggawa.
A halin yanzu kuma yace hukumar asibitin ta sanar da sashen dake bincike kan irin wadannan cutuka game da wannan maras lafiya wadda ta fito daga karamar hukumar Garum Malam.
Rahotanni sun bayyana cewa mijin maras lafiyar a yanzu shima yana karkashin kula ta musamman a wajen sashen kula da cutuka masu yaduwa.