• Home  
  • ‘Yan Sanda Sun Kamo ‘Yan Daba A Kano
- Babban Labari - Labarai

‘Yan Sanda Sun Kamo ‘Yan Daba A Kano

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta kama mutane 8 cikin wadanda ake zargi sun fito fadan daba tare da jiwa Kansu raunuka, a unguwar kofar Na’isa ranar Alhamis din data gabata. Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana a shafin sa na Facebook , ayau Asabar. Rundunar […]

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta kama mutane 8 cikin wadanda ake zargi sun fito fadan daba tare da jiwa Kansu raunuka, a unguwar kofar Na’isa ranar Alhamis din data gabata.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana a shafin sa na Facebook , ayau Asabar.

Rundunar yan sandan ta kuma bayyana damuwa, kan yadda matasan da suka samu raunukan, suka ki sanarwa da yan sanda, don kaisu asibiti a kula da lafiyarsu.

Kiyawa ya kara da cewa jami’an yan sanda sun shiga cikin unguwar, tare da mutane 8 da raunuka a jikinsu da kuma Wukake.

Sanarwar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike don kamo sauran wadanda ake zargi da aikata laifukan.

A ranar Alhamis din data gabata ne , wasu matasa da ake zargin Yan daba ne suka fito,Inda suka tayar da hankalin mazauna yankin da makotansu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai