Wani binciken da wata kafar yaɗa labarai ta yi a kan shafin Tiktok, ta gano cewa shafin na sa mutane yin wasu abubuwan na taɓara waɗanda suka saɓawa al’ada da kuma gurɓata ɗabi’unsu.
Binciken ya gano yadda shafin ke karfafa yaɗawa da bayyana ra’ayi a kan wasu batutuwa, wanda ke iya sauyawa ko ɓata tarbiyya a rayuwa ta yau-da-kullum.
Shafin na Tiktok na nuna wa mutane wasu irin nau’ikan bidiyo da ba don son rai ko zaɓinsu ba ne suke kallon su ba.
Sai dai shafin na Tiktok na cewa ya tsara ayyukansa ne ta yadda zai tabbatar da tsaro da kuma tafiya kan abin da ke jan hankali mutane ko suke tattaunawa ko faruwa.