Labarai

Babban Labari Labarai Labari Cikin Hoto Lafiya

An Kaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Ta Shafukan Sada Zumunta Kan Allurar Rigakafi.

  Daga: Zubaida Abubakar Ahmad A wani sabon yunƙuri na rage shakkun kan yiwa yara allurar rigakafi , masu ruwa da tsaki a jihar Kano sun ƙaddamar da wani gangami na jan hankali a ƙarƙashin shirin bayar da rigakafin da ake yiwa yara ta Najeriya (VaxSocial), tare da tallafin Save the Children. An kaddamar da […]

Babban Labari Labarai

An Dage Jana’izar Aminu Ɗantata Zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana’izar fitaccen ɗankasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa. Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya tabbatar wa da BBC ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina. ”Akwai ƙa’idoji da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan […]

Babban Labari Labarai

Iran Ta Ci Gaba Da Aikin Nukiliyarta

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da inganta sinadarin Uranium, mako guda bayan da Amurka ta haɗa hannu da Isra’ila wajen kai harin bama-bamai a manyan cibiyoyin nukiliyarta. Mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Majid Takht-Ravanchi ya shaida wa BBC cewa za a iya tattauna iya matakin da za a iya kai wa na […]

Babban Labari Labarai

Jana’izar Aminu Ɗantata: Abba Da Sarki Sanusi Sun Tafi Saudiyya

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sun tafi ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata. Gwamnan ya jagoranci tafiyar ce domin halarta Sallar Jana’izar a Madina ne, bayan rasuwar hamshaƙin attajirin a birnin Dubai da ke ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a […]

Babban Labari Labarai

Ya Kamata A Ba NJC Ikon Naɗa Shugaban INEC

A Najeriya yayin da zaɓen 2027 ke matsowa kusa wasu sun fara yin kiran karɓe ikon naɗa shugaban hukumar zaɓen ƙasar watau INEC daga hannun shugaban ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada. Masu irin wannan ra’ayi na ganin cewa hakan na kawo cikas ga ingancin zaɓen ƙasar, a don haka ya kamata […]

Babban Labari Labarai

Gobe Litinin Za A Yi Jjana’izar Marigayi Aminu Ɗantata A Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina. Mustapha ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta cewa, “Alhamdulillah an samu amincewar (hukumomi), za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa Madina. […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000