Labarai

Labarai

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen ƙasa a watan Janairun 2027, ana sa ran miliyoyin ‘yan ƙasa za su kaɗa ƙuri’a domin zaɓen shugaban ƙasa, gwamnoni, da kuma ‘yan majalisun dokoki na tarayya da na jihohi. Lokacin da ‘yan Najeriya suka je rumfunan zaɓe a shekarar 2023, mutane da dama sun yi imanin cewa […]

Babu Rukuni

Ba na nuna wa Kiristoci ƙiyayya — Sheikh Jingir

Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya musanta zargin nuna wa Kiristoci ƙiyayya. Sheikh Jingir, ya ce an yi wa kalamansa da ya yi a auren gata da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya, mummunar fahimta. Ya ce ba shi da nufin nuna ƙiyayya ko cin mutuncin Kiristoci da sauran […]

Labarai

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro Ƙungiyar Kanawa Mazauna Birnin Tarayya Abuja ta gudanar da wani babban taro a ranar Lahadi, wanda ya samu halartar shugabannin ƙungiyar daga ƙananan hukumomin birnin. Shugaban Kanawa Mazauna Abuja Initiative Group, Alhaji Ali Baba, ya ce wannan ne karon farko da ƙungiyar ta gudanar da irin wannan […]

Labarai

Rimingado ya kaddamar da kwamitoci 9 da kan yaki da miyagun kwayoyi a Kano.

Shugaban kwamitin haɗin gwiwar hukumomi ta yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi a Kano, Muhuyi Rimingado, ya ƙaddamar da kwamitoci tara domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi a jihar. Rimingado ya buƙaci mambobin kwamitocin da su kasance masu jajircewa, tare da aiki kafada da kafada wajen ganin an cimma manufofin rundunar. […]

Babban Labari

Jami’ar Sule Lamido ta ziyarci tashar MUHASA kan shirin bude sashen koyar da aikin jarida

Wakilai daga Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa sun kai ziyara tashar MUHASA Radio da Talabijin, a wani mataki na ƙoƙarin buɗe sashen koyar da aikin jarida a jami’ar. Farfesa Mustapha Dan Malam ne ya jagoranci tawagar, inda suka gana da shugabanci da ma’aikatan tashar domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi koyar da […]

Kasashen Ketare

Sakataren sojin kasan Amurka zai yi murabus

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito daga Mujallar Wall Street cewa ana sa ran Sakataren Rundunar Sojin Ƙasa ta Amurka, Dan Driscoll, zai yi murabus kafin ƙarshen shekara, bayan watanni ana samun takun-saka tsakaninsa da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth. Mujallar Wall Street Journal ta wallafa rahoton ne bisa bayanan wasu mutane da ke […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000