Home » Boko Haram Ta Kwace Makaman Sojoji Na Tiriliyoyin Naira: Yusuf Gadgi

Boko Haram Ta Kwace Makaman Sojoji Na Tiriliyoyin Naira: Yusuf Gadgi

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗaɗensu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas.

Gadgi ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan ƙudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga Jihar Borno ya gabatar a zauren Majalisar, kan gobarar da ta tashi a ma’ajiyar makamai ta rundunar soji da ke Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri da kuma ƙaruwar hare-haren Boko Haram a jihohin Borno da Yobe a baya-bayan nan.

Ɗan malisar ya ce yawan yadda ’yan ta’adda ke lalata kayan yaƙin sojoji a yanzu, ba a taɓa ganin irinsa ba a baya. Ya ƙara da cewa rashin ɗaukar mataki cikin gaggawa zai haifar da mummunan sakamako musamman ga zaɓaɓɓun shugabanni.

Ya ce, “Na firgita da abin da Boko Haram ta yi a Barikin Giwa da sauran cibiyoyin sojoji. Akwai abin damuwa game da tsaro da amincin ’yan Najeriya da ma ita kanta ƙasar.”

Yusuf Gadgi ya ce Majalisa ta ware wa sojoji kuɗaɗe a cikin kasafi domin sayen motocin yaƙi sama da 40 da sauran kayan yaƙi, da kuɗinsu ya kai tiriliyoyin naira, domin tsaron ’yan Najeriya.

Ya ce. “To yaya za mu samu tabbacin tsaron al’umma a irin wannan yanayi, idan ’yan ta’dda sun kwace waɗannan kayan yaƙi?”

Ya ci gaba da cewa “Majalisa tana yin iya bakin ƙoƙarinta wajen yin magana da kan sha’anin tsaro, amma wajibi ne hukumomin gwamnati su ɗauki mataka. Ya zama tilas shugaban ƙasa ya binciki shuagabannin sojoji da sauran hukumomin tsaro game da wannan sakacin, sannan ya ɗauki mataki a kansu.

“Sannan ya zama dole mu gayyaci hukumomin gwamnati domin su rika bayani a game da gazawarsu wajen gudanar da ayyukansu,” in Honorabul Yusuf Gadgi.

Ya bayyana cewa yawan halin ko-in-kula daga gwamnati da hukumomin tsaro zai haifar da rashin yardar al’umma da su, wanda hakan babbar barazana ce ga shugabannin siyasa.

Ya ce ya zama wajibi a ɗauki mataki, idan ba haka ba, “’yan Najeriya za su ɗauki matakan kare kansu da kansu, kuma za su yake mu kamar yadda za su yakar Boko Haram.”

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?