Home » KSCHMA Ta Jaddada Kudirin Rage Yawan Mutuwar Kananan Yara A Kano

KSCHMA Ta Jaddada Kudirin Rage Yawan Mutuwar Kananan Yara A Kano

Da take jawabi ga manema labarai a birnin Kano, Babbar Sakatariyar KSCHMA, Dakta Rahila Aliyu Muktar ta bayyana bukatar gaggawa na mayar da hankali kan lafiyar uwa da jariri a karkashin tsarin “Universal Health Coverage (UHC)”. Ta ce: “Ta hanyar KSCHMA, za mu iya ceton rayukan yara ta hanyar kawar da bambancin samun kulawa daga rashin kudi.”

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Hukumar Kula da Tsarin Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) ta sake jaddada kudirinta na ceton rayukan mata da kananan yara ta hanyar kawar da bambancin samun kulawar lafiya, musamman wajen rage yawan mace-macen yara ‘yan kasa da shekara biyar a fadin jihar.

Da take jawabi ga manema labarai a birnin Kano, Babbar Sakatariyar KSCHMA, Dakta Rahila Aliyu Muktar ta bayyana bukatar gaggawa na mayar da hankali kan lafiyar uwa da jariri a karkashin tsarin “Universal Health Coverage (UHC)”. Ta ce:

“Ta hanyar KSCHMA, za mu iya ceton rayukan yara ta hanyar kawar da bambancin samun kulawa daga rashin kudi.”

KSCHMA, ta hanyar manyan shirinta irin su Basic Healthcare Provision Fund (BHCPF) da Shirin Tallafawa Marasa Galihu (VPP), ta samu nasarori masu yawa wajen tabbatar da cewa mata masu juna biyu, jarirai da yara ‘yan kasa da shekara biyar—musamman daga gidajen talakawa da yankunan karkara—na samun kulawa ta lafiya kyauta kuma mai inganci a fiye da cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko (PHCs) a fadin jihar.

Muhimman Abubuwan Da Aka Cimma Daga 2023 zuwa 2025:

Sama da ziyara 43,000 na duba lafiya ga mata masu juna biyu

Fiye da haihuwa 10,000 cikin kwanciyar hankali, ciki har da fiye da 300 na tiyata (cesarean)

Kulawa na fiye da mata da yara 734,000 kan cutar zazzabin cizon sauro.

Rigakafin yara ‘yan kasa da shekara biyar fiye da 43,000

Kula da dubban matsalolin gaggawa da suka shafi yara, ciki har da gudawa da matsalolin numfashi

Wadannan ayyuka duka ana biyan su gaba daya ga wadanda suka cancanta karkashin shirye-shiryen KSCHMA, domin tabbatar da cewa rashin kudi ba zai sake zama cikas ga samun kulawa da zata ceci rai ba.

Dakta Muktar ta kara da bayyana cewa KSCHMA na hada shirin tsara iyali, tallafin gina jiki, da lura da inganta lafiyar jiki cikin ayyukan lafiyar uwa da jariri domin kara inganta rayuwar yara.

“Ba kawai maganar kiwon lafiya muke ba—muna maganar adalci da daidaito a cikin al’umma. Kowane yaro, komai matsayin iyayensa, yana da hakkin samun ingantacciyar kuruciya a rayuwa,” in ji ta.

KSCHMA na ci gaba da aiki tare da abokan hadin gwiwa, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, masarautun gargajiya da kungiyoyin al’umma domin tabbatar da cewa kulawar lafiya ta kai kowane yanki na Jihar Kano.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?