Home » An Shirya Zaman Horas Da Masu Yada Aiyukan Gwamnatin Kano A Shafukan Sada Zumunta

An Shirya Zaman Horas Da Masu Yada Aiyukan Gwamnatin Kano A Shafukan Sada Zumunta

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano, tare da hadin gwiwar NEXA, sun shirya taron horas wa na wuni biyu ga wadanda suke yada manufofi da aiyukan gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a shafukan sada zumuntar, Facebook, X, Instergram, dabarun yadda za su yi amfani da shafukan ta hanyar bin dokoki da kuma tantance labaran karya don tsaftace harkar baki daya.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa sun gayyaci kwararru don horas da matasan da suka gayyata kan yadda za su kaucewa cin mutuncin mutane a shafukan sada zumunta.

Waiya ya kara da cewa, daman suna da wani zaure na ma’abota shafukan sada zumunta don yada aiyukan gwamnatin Kano, inda suka dacewar hadasu wuri guda don horaswa da su dabarun yadda yakamata su gudanar da aiyukansu.

‘’ za mu koyar da su yadda ake amfani da shafukan sada zumunta da kuma yadda zaka samar da labari na gaskiya don isarwa ga al’umma da kuma kaucewa yada labaran karya’’ Waiya’’.

Ya ce suna fatan bayan kammala samun horon na wuni biyu za su samu kwarewa kan wadda suke da ita don inganta aikinsu wajen kawo rahotannin aiyukan gwamnatin Kano.

Wasu daga cikin mahalatta bitar sun bayyana gamsuwarsu kan horaswar, tare da cewa zai kara tsaftace harkar musamman yadda ake samun wasu suna cin mutuncin mutane a shafukan sada zumunta .

Taron dai an gudanar da shi ne a sabuwar jami’ar Bayero Kano, inda ya samu halattar jama’a daga sassa daban-daban.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?