Hukumar Ƙwallon Ƙafar Afirka (CAF) ta sanar da soma bincike dangane da hargitsin da aka yi bayan tashi daga wasan kwata-final na Gasar Kofin Afirka AFCON da aka fafata tsakanin Nijeriya da Algeria.
CAF a wannan Litinin ɗin ta ce ta soma binciken wanda kuma za ta ɗauki matakan ladabtarwa kan abin da ta kira “abin da bai dace ba” da aka gani bayan tashi daga wasan na ranar Asabar.
Wata sanarwa da CAF ta fitar, ta ce ta miƙa lamarin zuwa kwamitin ladabtarwa domin bincike, tare da jaddada cewa za a ɗauki matakin da ya dace idan aka samu waɗanda aka tabbatar da laifinsu.
Bayanai sun ce hargitsi ya ɓarke ne a filin wasa bayan tashi daga wasan da aka buga a birnin Marrakesh a ranar Asabar, inda Najeriya ta doke Algeria da ci 2–0, bayan ƙwallayen da Victor Osimhen da Akor Adams suka zura bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa duk wani matakin ladabtarwa da CAF za ta ɗauka na iya shafar tawagar Super Eagles yayin da suke shirin karawa da Morocco mai masaukin baƙi a wasan kusa da ƙarshe da za a buga ranar Laraba.
Sai dai CAF ta ce tana kuma binciken wasu abubuwan da suka faru a wasan daf da na kusa da ƙarshe da aka buga ranar Juma’a tsakanin Morocco da Kamaru.
Tawagar Morocco ce ta yi nasara a wasan da ci 2–0 a Rabat, amma ’yan wasan Kamaru suka nuna rashin jin daɗinsu kan yadda aka yi alƙalancin wasan, musamman rashin samun bugun fanareti bayan ƙeta da aka yi wa ɗan wasan Manchester United, Bryan Mbeumo a cikin da’irar yadi na 18 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
