Labarai

An Yi Girgiza A  Gwamnatin Kano

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauke sakataran gwanatin jihar Dokta Abdullahi Baffa Bichi da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Shehu Wada Sagagi an kuma sauke kwamishinoni 5. Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daractan yaɗa labaran gwamnan na Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa. Baya ga haka gwamnan […]

Read more

Naja’atu da Bafarawa Sun kafa Sabuwar Tafiyar Matasa

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarwa da kuma fitacciyar ‘ƴar gwagwarmaya a Arewacin Najeriya, Hajiya Naja’atu Muhammad, sun ƙaddamar da wata sabuwar tafiyar matasa don ceto yankin Arewacin Najeriya me suna Northern Star Youth Movement Initiative (NSYMI). A jawabinsa, Bafarawa wanda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ne a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya ce, lokaci ya […]

Read more

Isra’ila Ta Kai Hare-hare 300 Syria

Rahotanni sun nuna cewa jiragen saman Isra’ila sun kai ɗaruruwan hare-hare ta sama a Syria, ciki har da Damascus babban birnin ƙasar. Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) mai mazauni a Birtaniya ta tattara sama da hare-hare 310, waɗanda dakarun IDF suka kai tun bayan kifar da gwamnatin Assad a […]

Read more

An kama Wani Dillali Da Kayan Tallafin Manoma A Jigawa

Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa na Karamar Hukumar Kiyawa jihar Jigawa ya shiga hannu, kan badaƙalar kayan noman da Gwamnatin Tarayya ta ba wa manoma a farashi mai rahusa. Da yake bayyana cewa za su fuskanci fushin doka ya bayyana takaici bisa yadda almundahanar ta dabaibaye shirin Gwamnatin Tarayya na bunƙasa noma da tallafa wa […]

Read more