An kama Wani Dillali Da Kayan Tallafin Manoma A Jigawa

Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa na Karamar Hukumar Kiyawa jihar Jigawa ya shiga hannu, kan badaƙalar kayan noman da Gwamnatin Tarayya ta ba wa manoma a farashi mai rahusa.

Da yake bayyana cewa za su fuskanci fushin doka ya bayyana takaici bisa yadda almundahanar ta dabaibaye shirin Gwamnatin Tarayya na bunƙasa noma da tallafa wa manoma da kayan noma a jihar.

A yayin da gwamnan yake rangadi a cibiyoyin rabon kayan noma a jihar ne ya bankaɗo yadda dillalai da jim’an gwmanati suke zagon ƙasa ga shirin.

Gwamnan ya ce, “Dillalai na zagon ƙasa ga wannan shiri, wanda hakan ke kawo wa manoma matsala wajen ci gaba da noma su. Ba za mu lamunci hakan ba,” in ji gwamnan.

Ba Za Mu Ragawa Tinubu A 2027 Ba-Atiku

Ya bayyana cewa “gwmanati ta sanya N159,187 a matsayin kuɗin kayan noman, wanda ta rage rabin kuɗinsa ga manoma

“Amma mun samu bayanai cewa ’yan kasuwa na ƙara musu N5,000 zuwa N10,000, wanda ƙarin nauyi ne ga manoma.

“Wannan zagon ƙasa ne ga ƙoƙarin gwamnati na tallafa wa harkar noma da manoma. Don haka za mu tabbatar an ƙwato duk haramtattun kuɗaɗen da aka karɓa a hannun manoma, a mayar musu,” a cewar Gwamna Namad

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.