Lamiɗo Ya Zama Sarkin Ƙananan Hukumomi 3  Maimakon 8

Gwamantin Jihar Adamawa ta tabbatar da ta ƙwace ikon naɗa wa da tsige sarakuna daga hannun  Lamiɗon Adamawa, Alhaji Mustapha Barkinɗo ta damƙa wa Gwamnan Jihar.

Haka zalikaɓgwamnatin ta tsige Lamiɗo daga matsayinsa na Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar na dindindin.

Majalisar Dokokin Adamawa ce dai ta yi wa dokar masarautun jihar garambawul a ranar Laraba, haka kuma ta rage ƙasar Masarautar Lamiɗon Adamawa daga ƙananan hukumomi takwas zuwa uku: Girei da Jimeta da kuma Yola.

Dokar, majalisar ta ce za ta tabbatar da adalci a tsakanin masarautun jihar da kuma kare tarihi da al’adu.

Post masu alaƙa

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi