Shugaban Ƙasar Turkiyya Ya Sake Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa
A karon farko da ƙasar Turkiya ke zuwa zagaye na biyu a zaben shugaban kasa, bayan da shugaba Erdogan ya gaza kawo kashi 50 na kuri’un da aka kada makwanni 2 da suka gabata, duk da cewa shi ke da mafi yawan kuri’un da aka kada a tsakanin ‘yan takarar na wancan lokaci.