‘Yan Fashin Daji Sun Saki Wasu DalibaI 4 Na Sakandiren Yawuri
Shugaban ƙungiyar iyayen ɗaliban da suka rage a hannun ‘yan fashin daji, Salim Ka’oje ne ya tabbatar da haka, inda ya ce ‘yan matan huɗu sun kuɓuta ne sanadin wani ƙoƙari da mahaifan ɗaliban da kuma masu tallafa musu suka yi.