Kano: INEC Ta Cire Sunan Alhassan Ado Doguwa Daga Jerin Sunayen Zababbun ‘Yan Majalisa

Alhassan Ado Doguwa

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta cire sunan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, daga jerin wadanda suka lashe zaben da aka gudanar a makon jiya.

A yayin da INEC ke shirin mika wa wadanda suka ci zaben kujerar sanata da na majalisar tarayya takardun shaida, MUHASA ta gano cewa hukumar ba ta sanya sunan Alhassan Doguwa ba a matsayin zababben dan Majalisar Tarayya na mazabar Doguwa/Tudun Wada.

Wannan na zuwa ne duk da cewa Baturen zaɓen hukumar, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya sanar cewa Alhassan Ado Doguwa na Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben a mazabarsa da kuri’a 39,732, a yayin da babban abokin karawarsa, Yushau Salisu Abdullahi na Jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 34,798. Amma a cikin jerin sunayen da INEC at fitar a daren jiya Litinin na wadanda za a mika wa shaidar cin zabe, babu sunan Alhasannan Ado Doguwa

Alhassan Ado Doguwa

Daga bisani hukumar ta bayyana cewa tursasa wa baturen zabenta aka yi ya sanar da sakamakon zaben da ke nuna dan majalisar ya lashe zaben ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Mun yi kokarin samun karin haske daga hukumar, reshen Jahar kano ama hakan mu bai cimma ruwa ba.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr