Labarai

DSP Hussaini Abdullahi Ya Zama Sabon Mai Magana Da Yawun Rundunar Yan Sandan Shiya Ta Daya Zone One Kano.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da naɗe-naɗen sabbin masu magana da yawun rundunar wasu shiyyoyi, ciki har da naɗin DSP Hussaini Abdullahi a matsayin sabon mai magana da yawun rundunar yan sandan shiya ta daya wato Zone 1, Kano. DSP Hussaini Abdullahi, wanda ya maye gurbin CSP Bashir Muhammad, ya kasance mataimakin kakakin rundunar […]

Read more

Gwamnan Kano zai samar da jirage marasa matuƙa kan tsaro

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin samar da jirage marasa matuƙa da sauran kayan aikin tsaro domin sa ido da kuma ɗaukar mataki cikin gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankunan iyakar Kano da Katsina. Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin […]

Read more

Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro

Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, a zamanta na yau Laraba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga ofishin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele. Sanarwar ta ce majalisar ta karɓi buƙatar Shugaban Ƙasa Tinubu na tabbatar […]

Read more

Gwamnan Abia ya ziyarci Tinubu a Villa

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya ziyarci Shugaba Tinubu a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja. Duk da cewa babu cikakken bayani game da ziyarar, wasu a ƙasar na ganin ba ta rasa nasaba da batun shugaban ƙungiyar ƴan awaren Biafra, Nnamdi Kanu da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da rai cikin watan da ya […]

Read more

Tinubu ya ganawa da manyan hafsoshin tsaron ƙasar

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Villa. Manyan hafsoshin sun isa fadar shugaban ƙasar da maraicen yau Talata, inda suka yi ganawa har ta tsawon sa’o’i uku, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito. Ba a dai bayyana dalilin ganawar ba, amma wasu na ganin […]

Read more

Majalisar Dattawa ta yi sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta

Majalisar Dattawa ta sanar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta, musamman na tsaro da na tattara bayanan sirri sakamakon ƙalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga kwamitin zaɓe na Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio. A sabon tsarin, Sanata Yahaya Abdullahi […]

Read more