‘Babban sufeton ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya yi murabus’

Babban sufeton ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya sauka daga muƙaminsa.

Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta shaida wa BBC cewa Kayode Egbetokun ya ajiye aikinsa ne a ranar Talata.

Har zuwa yanzu, rundunar ƴansandan ƙasar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce game da makomar shugabancin rundunar, kodayake babu cikakken bayani a hukumance kan dalilin ajiye aikin.

A watan Yunin 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da Kayode Egbetokun a matsayin wanda yake son naɗawa muƙamin sufeta-janar na ƴansandan ƙasar, inda a ƙarshen watan Oktoban shekara ta 2023 Majalisar ƴandsanda ta ƙasar ta tabbatar da nadin nasa.

Post masu alaƙa

Ana zargin mahaifi da kashe ’yarsa kan auren dole a Katsina

An kama mutum 2 kan zargin sayar da filayen gwamnatin a Kano

Waɗanda suka sace ɗaliban Oyo sun buƙaci musaya da manyansu muka ƙi’