Labarai

Yan Bindiga Sun Sace Mata 5 A Kano

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari garin Ƴankwaɗa da ke Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata shida ciki har da masu shayarwa, tare da harbin mutum ɗaya. Wannan na zuwa ne mako guda bayan kai irin wannan harin a wasu kauyuka a ƙananan hukumomin […]

Read more

Charles Soludo Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Anambra

Hukumar zaɓen mai zaman kanta INEC ta sanar da Charles Soludo na Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba. Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da […]

Read more

Tinubu Ya Gana Da Shugaban Ƙasar Saliyo A Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da takwaransa na ƙasar Saliyo, Shugaba Julius Maada Bio, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, da yammacin Juma’a. Shugaba Bio ya isa fadar Villa da misalin ƙarfe 9:08 na dare, inda aka yi masa tarɓar ban girma, kafin ya wuce ofishin Shugaba Tinubu domin gudanar da ganawar […]

Read more

Sanata Barau Jibrin Zai Yi Karar Wani Tsagin APC Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin (CFR), ya bayyana shirinsa na kai ƙarar kwamitin yaƙin neman zaɓen Gawuna-Garo bisa zargin cewa shi da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, sun karɓi cin hancin dala miliyan 10 domin hana tabbatar da naɗin Abdullahi Garba Ramat a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa […]

Read more

Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a. Sarkin Musulmi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya gana da Shugaban Ƙasa ba tare da ’yan jarida ba. Ganawar na zuwa ne kwanaki kaɗan […]

Read more