An kai hari gidan jami’in ɗan sanda a Yobe

Wasu mahara da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari gidan babban Jami’in kula da ofishin ‘yan sandan na Tattaɓa, ASP Mohammed Modu, da ke yankin Bara a ƙaramar hukumar Gulani, Jihar Yobe.

Kamar yadda rahoton Jami’an tsaro ke nunawa cewa, da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar daren ranar 9 ga Disamba, maharan suka mamaye gidaje uku na jami’in, suka sace babur ɗinsa na Haojue da kekuna uku da mota ƙirar Golf 3, da sauran kayansa kafin su ƙona gidaje uku da motar Honda Civic.

An yi zargin cewa, wani mai kai rahoto ne ga ‘yan ƙungiyar da ke cikin al’ummar wannan yankin ya bada rahoton Jami’in ga waɗannan maharan.

Jami’an tsaro sun ziyarci wurin da lamarin ya faru kuma sun tattara bayanai game da ɓarnar, ba tare da an samu rahoton asarar rayuka ba.

An shawarci jami’in da ya yi taka-tsantsan yayin da ake ƙara tsaurara sa ido da sintiri a yankin don hana sake kai hari a yankin.

Post masu alaƙa

Dangote, Habasha da Djibouti za su gina bututun mai na dala miliyan 600

Atiku ya naɗa El-Rufai cikin mambobin kwamitin yaƙin zaɓensa

Sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa na haifar da sakamako mai kyau – Shettima