DSS ta kama waɗanda ake zargi da sace Farfesa A Nasarawa

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, DSS, ta ceto shugaban sashin tsangayar Noma ta Jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi, Farfesa Samuel Okunsebor, bayan da wasu yan bindiga sun yi garkuwa da shi.

Rahotanni sun ce an sace Farfesan ne ranar Laraba a tsakanin ƙananan hukumomin Lafia da Nasarawa Eggon dake Jihar.

Jami’an DSS sun ceto shi a juma’arnan da rana, kafin daga bisani su miƙa shi ga iyalansa, bayan kai shi Asibitin koyarwa na jami’ar tarayya da ke Lafia domin duba lafiyarsa.

Hukumar DSS ta kuma cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a shirya sace Farfesan, inda ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.

Wani babban jami’in jami’ar jihar Nasarawa ya yabawa DSS bisa ƙoƙarin da ta yi wajen ceto Farfesan cikin gaggawa, yana mai cewa jami’ar na matuƙar godiya da wannan nasara.

Ya ƙara da cewa suna da yakinin cewa waɗanda aka kama za su fuskanci hukunci  da zarar an kammala gudanar da bincike.

Post masu alaƙa

An gurfanar da waɗanda ake zargi da sace ɗaliban Oyo

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi