Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kashe kusan Naira bakwai (7) a karkashin Shirin Tallafa wa Ma’aikatan Gwamnati ta Fuskar Noma (JSWAP), inda sama da ma’aikatan gwamnati 17,000 suka ci gajiyar shirin tun daga mataki na farko zuwa na uku.
An bayyana hakan ne yayin kaddamar da rabon kayan aikin noma na kashi na hudu na daminar shekarar 2026 a Dutse.
Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, ta bakin Mataimakinsa, Injiniya Aminu Usman, ya ce shirin na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa na inganta rayuwar ma’aikata, bunkasa harkar noma da tabbatar da wadatar abinci.
Shugaban Majalisar Tattaunawar Ma’aikatan Gwamnati (JPSNC), Kwamared Yusha’u Abubakar, ya yabawa gwamnatin jihar bisa jarin da ta zuba a shirin, yana mai cewa tsarin mayar da rancen ya tabbatar da dorewar shirin tare da bai wa karin ma’aikata damar cin gajiyarsa a kowace damina.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya ce nasarar dawo da kudaden rancen da aka bayar a baya ta ba da damar ci gaba da gudanar da shirin cikin tsarin asusun juyin juya hali (revolving fund) ba tare da tsaiko ba.
A ƙarshe an kammala taron da rabon kayan aikin noma ga ma’aikata masu cin gajiyar shirin na daminar 2026, yayin da gwamnati ta jaddada kudurinta na ci gaba da tallafa wa ma’aikata, bunkasa noma da karfafa tattalin arzikin jihar

Post masu alaƙa

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama dan bindiga da sanye da kayan sojoji.