Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Alhaji Nura Umar Bungudu, bayan sun kai hari gidansa cikin dare a ranar Alhamis.
Rahotanni sun ce maharan sun kawo harin ne har cikin garin Bungudu, inda suka nufi gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke unguwar Zango, kusa da Gusau.
Wata majiya ta ce maharan sun kashe ’yan sanda biyu da jami’an sa-kai biyu bayan sun yi artabu da jami’an tsaron da ke gadin gidan, sannan suka yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar tare da matarsa da ’ya’yansa.
Sai dai jami’an tsaro sun samu nasarar ceto wasu daga cikin yaran yayin da suke bibiyar maharan, amma har yanzu shugaban ƙaramar hukumar na hannun masu garkuwa da mutanen.
Majiyar ta ce wasu ƙarin jami’an tsaro sun kawo ɗauki gidan shugaban ƙaramar hukumar bayan maharan sun tsere.
Ta kuma zargi masu bai wa ’yan bindiga bayanan sirri da kuma amfani da manyan makamai da taimaka musu wajen kai irin waɗannan hare-hare.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba, domin ba a samu jin ta bakin kakakinta, DSP Yazid Abubakar ba.