Babban Labari

Jamiyyar APC ta yi wa gwamnan Ribas rajista a hukumance

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya samu rijistar zama ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar a gidan gwamnati da ke Fatakwal. Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, Tony Okocha, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya miƙa katin ga Fubara a ranar Juma’a da […]

Read more

Amurka ta kama jirgin man fetur na Najeriya

Wani babban jirgin ruwan ɗauke da danyen mai (Super Tanker) wanda ya tashi daga Najeriya zuwa Amurka an kama shi saboda zargin ya ɗauke da danyen mai da aka sace. Hukumomin Amurka na gudanar da bincike, inda ake zargin jirgin na da alaƙa da safarar muggan ƙwayoyi da ayyukan fashi a teku. Jirgin mallakar ɗan […]

Read more

2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe

Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanninta a Jihar Gombe, inda ta jaddada muhimmancin haɗin kai da farfado da jam’iyyar tun daga matakin ƙananan hukumomi zuwa jiha gabanin zaɓen 2027. Taron ya halarta bayan zuwan wakilai daga dukkanin ƙananan hukumomin jihar. Mambobin jam’iyyar sun yaba da yadda komai ya gudana cikin lumana da tsari, abin […]

Read more

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 3 A Binuwai

Dakarun Sojin Operation Whirl Stroke (OPWS), sun kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Binuwai. Mai magana da yawun OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ya ce sojojin sun samu bayanan sirri kuma suka yi aiki tare da ’yan sandan […]

Read more