Gwamna Radda Ya Dora Harsashin Gina Ma’aikatar Sarrafa Rogo a Kastina

Gwamnan Jihar Katsina ya kafa harsashin ginin masana’antar sarrafa rogo domin samar da isashen garin kwaki da ake kawo wa daga kudancin Najeriya.
Manufar kafa kamfanin shi ne sauƙaƙawa al’umma wahalar da suke sha wajen sayen garin kwaki duk da cewa su ke noma rogo amma sarrafa shi ne yana basu wahala.
Haka kuma Gwamna Radda ya lura cewa masu noman rogo a yankin Batsari suna shanya shi ne a kan tituna wanda hakan ke da illa, musamman ga yara da kuma tsofaffi.
Da yake jawabi a wajen kafa harsashin kamfanin, a ƙaramar hukumar Batsari Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya ce haka zai tallafa wa masu ƙananan sana’o’i wajen bunƙasa tattalin arzikin su.
A cewar shi, lokacin yakin neman zabe ya lura da cewa ƙaramar hukumar Batsari na daga cikin wuraren da ake noman rogo sosai wanda al’umma ke samar da rogo mai taren yawan.
A ƙarshe ya ce, mutanen Batsari sun daɗe da wannan sana’a ta noman rogo tun Iyaye da kakanni, wanda ya ce haka ta sanya ya bai wa hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitun sana’o’i umarnin kafa masana’antar sarrafa rogo a Batsari.

Post masu alaƙa

Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika

Dalilin da ya sa na gina Masallatai 50 da aurar da marayu 10 — Mataimakin Gwamna

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari