Gwamnatin Najeriya ta umarci babban bankin kasar CBN da ya gaggauta sakin tan miliyan 500 na masarar da ya saya daga hannun manoma domin amfanin jama’a, sakamakon tsada da kuma karancin abincin da ake fuskanta a sassan kasar.
Wannan umarni ya biyo bayan matsayin da majalisar tattalin arzikin kasar ta dauka lokacin da ta gudanar da taron ta, a karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Majalisar wadda ta kunshi gwamnonin jihohi, ta bayyana matukar damuwar ta da irin halin da jama’ar kasar suka samu kan su, sakamakon tsadar abincin.
Wannan ne sanya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta baci akan abinci.
Yan Najeriya sun zuba ido suga yadda za’a raba abincin da kuma fatar ganin gwamnati ta tashi tsaye domin ganin wadanda akayi domin su sun samu abincin.