Rundunar Sojin Nijeriya ta sake aika karin sojoji zuwa Jihar Filato da ke yankin tsakiyar kasar, don kwantar da tarzoma a yankunan.
Mahukunta sun ce cikin watanni uku da suka gabata, an kashe akalla mutane 300 sakamakon rikicin kabilanci.
Tun watan Mayu ake ta samun rikice-rikice a Jihar Filato tsakanin Musulmai makiyaya da manoma Kiristoci.
Ana yawan samun barkewar rikici a Jihar Filato, lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.
Gwamann jahar ta filato Caleb Muftwang yace an tabbatar da kashe sama da mutane 300 yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba bayan ya gana da jami’an soji.
Rundunar sojin ta bayyana dauke helkwatar ‘Operation Safe Haven’ daga Jos babban birnin jihar zuwa yankin Mangu, daya daga cikin yankunan da aka fi samun rikicin.