An kiyasta Yawan harajin da Nijeriya ta karba ya kai naira tiriliyan 5.5, kwatankwacin dala biliyan bakwai kenan daga watan Janairu zuwa Yunin 2023 wanda shi ne mafi yawa da aka taba samu cikin wata shida.
Hukumar tattara kudin haraji ta kasa FIRS ta bayyana haka ne , a yayin da gwamnatin kasar ke daukar matakan karbar harajin a dukkan fannoni domin karfafa tattalin arzikinta.
Shugaban hukumar tattara haraji ta tarayya FIRS Muhammad Nami, ya yi hasashen cewa harajin da za a karba a shekarar 2024 zai kai naira tiriliyan 25, wato dala biliyan 31.6 kenan, inda zai ninka yawan na 2022 sau biyu.
Nijeriya ta shirya yi wa tsarin karbar harajinta garanbawul, wanda mutane ba sa son bayarwa, sannan ta fadada dabarunta ta hanyar kawar da duk wasu abubuwa da ke jawo mata tarnaki wajen cimma a kalla kashi 18 cikin 100 na samun harajin da zai shiga ma’aunin tattalin arziki na GDP cikin shekara uku.