• Home  
  • Cikin Hotuna: Yadda Hukumomin Tsaro Suka Yi Shirin Bayar Da Tsaro A Kano
- Babban Labari

Cikin Hotuna: Yadda Hukumomin Tsaro Suka Yi Shirin Bayar Da Tsaro A Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaron jihar, sun tabbatar da cewa za su bayar ingantaccen tsaro a lokutan bukukuwan sallah da kuma bayan ta. Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kwamishinan yan sandan jihar , CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya jagoranci tawagar […]

Rundunar yan sandan jihar Kano, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaron jihar, sun tabbatar da cewa za su bayar ingantaccen tsaro a lokutan bukukuwan sallah da kuma bayan ta.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kwamishinan yan sandan jihar , CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya jagoranci tawagar hukumomin tsaron, wajen yin kewaye a sassan birnin jihar.
Gamayyar hukumomin sun hada da, yan sanda, Sojoji, DSS, Civil Defense, hukumar shige da fice, jami’an gidan gyaran hali , NDLEA da kuma hukumar kiyaye afkuwar hadura FRSC.

Kwamishinan yan sandan ya taya al’ummar musulmi, murnar bikin salla karama, tare da tabbatar musu cewa kowa zai gudanar da shagulgulan sallah lafiya ba tare da wani razani ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai