Cin zarafin da Babban Jami’an tsaro (CSO) na Gwamnan Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba ya yi ga wakilin Talabijin NTA da ke Damaturu, Babagana Kolo a harabar Majalisar Dokokin Yobe da ke Damaturu a ranar Alhamis ya tada ƙura.
Lamarin ya faru ne yayin da wasu ’yan jarida ke jiran a shigar da su cikin zauren domin su bayar da rahoto kan gabatar da kasafin kuɗin 2026 da Gwamna Mai Mala Buni ya yi a gaban Majalisar Dokokin.
Shaidu sun ce Babban Jami’in tsaro (CSO) na fadar gwamnatin Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba, ya afka wa Kolo ya buge shi a fuska, lamarin da ya yi sanadiyyar raunuka a bakinsa da wasu ɓangarorin jikinsa.
An ruwaito cewa, lamarin ya kawo cikas ga yadda kafofin yaɗa labarai ke yaɗa labaran taron yayin da ‘yan jarida ke barazanar ƙauracewa gabatar da kasafin kuɗin.
Sai da Kwamishinan Yaɗa labarai, Alhaji Abdullahi Bego ya sa baki kafin ‘yan jaridar su ci gaba da ayyukansu.
